Hukumar kula da ’yan sama jannati na kasar Sin ko CMSA ta ce an yi nasarar harba kumbon Shenzhou-19 mai dakon ’yan sama jannati.
A ranar Laraba ne kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou-19 mai dakon ’yan sama jannati, inda ta aika da ’yan sama jannati uku, ciki har da mace injiniyan sararin samaniya ta farko ta kasar, zuwa falakinsa a tashar sararin samaniya don gudanar da aikin watanni shida.
CMSA ta ce, kumbon wanda aka dora a jikin rokar Long March-2F, ya cilla sama ne da misalin karfe 4 da minti 27 na safe agogon Beijing, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. Kana, kimanin mintuna 10 da harbawa, kumbon Shenzhou-19 ya rabu da rokar, kuma ya shiga falakinsa kamar yadda aka tsara, a cewar CMSA.
Sannan, CMSA ta sanar da cewa, kumbon ya yi kewaye-kewayen da ka tsara kuma ya sauka a gaban tashar sararin samaniya ta Tianhe da misalin karfe 11 na safe agogon Beijing. ’Yan sama jannatin guda uku dake cikin kumbon daga bisani sun shiga cikin na’urar Tianhe inda suka hadu da ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-18 dake jiran isowarsu. (Mohammed Yahaya)