Sufeto-Janar na ‘Yansandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya umarci dukkanin jami’an ‘yansanda a Nijeriya su sanya bakin kyalle na tsawon kwanaki bakwai domin girmama marigayi Babban Hafsan Soji, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya rasu.
Wannan matakin, kamar yadda kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana matakin a matsayin girmamawa jarumtar Lagbaja da jajircewarsa wajen yaki da ‘yan ta’adda a Nijeriya.
- Makinde Ya Amince Da N80,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashin Ma’aikata
- Mene Ne CIIE Ke Kawowa Kamfanonin Kasashen Waje?
Laftanar Janar Lagbaja, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yuni 2023, ya rasu yana da shekaru 56 bayan fama da rashin lafiya.
Baya ga umarnin Sufeto-Janar, Shugaba Tinubu ya kuma umarci a yi kasa-kasa da tutocin Nijeriya tsawon kwanaki bakwai.
Uwargidan Tinubu, Remi Tinubu ta ziyarci iyalan Lagbaja da yammacin ranar Laraba, domin yi musu ta’aziyyar rashin da suka yi.