Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar a yau Alhamis cewa, alkaluman farashin kayayyakin masarufi na kasar, abin da ake amfani da shi a matsayin ma’aunin raguwar darajar kudi, ya karu da kashi 2 cikin 100 a shekarar 2022.
Babbar jami’ar kididdiga ta hukumar NBS Dong Lijuan ta bayyana cewa, a cikin watan Disamba, farashi bai sauya ba, sakamakon kokarin da kasar Sin ta yi, wajen daidaita matakan dakile annobar COVID-19, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, baya ga matakan da aka dauka na tabbatar da samar da kayayyaki a kasuwanni da daidaita farashi.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)