Ranar 10 ga watan Yuni rana ce ta cudanyar wayewar kai, wadda kasar Sin ta gabatar da shawarar kebewa, sa’an nan babban zauren Majalissar Dinkin Duniya ya zartas da shawarar a kwanan baya.
To, me ya sa ake son kebe wannan rana don yayata tunanin yin cudanya tsakanin wayewar kai daban daban? Saboda kasa samun cudanya tsakanin mabambantan wayewar kai da al’adu, har ma da barkewar rikici tsakaninsu, sun zama ruwan dare a zamanin da muke ciki, lamarin da ya sa ake bukatar karfafa cudanya don neman shawo kan yanayin da ake ciki.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Kari Sansanin Sojoji A Neja
- UNAOC Ya Yi Maraba Da Kudurin Da Sin Ta Gabatar Na Ayyana Ranar Tattaunawa Tsakanin Mabambantan Al’ummomi Ta Duniya
Misali, matakan soja da kasar Isra’ila ke aiwatarwa a zirin Gaza sun haddasa asarar rayukan Falasdinawa fiye da 37000, galibinsu fararen hula, wadanda ba su san hawa ba balle ma sauka, amma duk da haka, Isra’ila din na ci gaba da kai hare-hare ga Gaza. Dangane da batun, yawancin kasashe sun bukaci a tsagaita bude wuta nan take, sai dai kasashe ’yan kalilan sun nuna goyon baya ga Isra’ila, wai tana da hakkin “kare kai”. Hakika, a idanun wadannan kasashe, bambancin wayewar kai da al’adu ne ya tabbatar da manufarsu ta shata layi tsakanin abokan gaba da kawaye, maimakon adalci, da da’a, da tausayin dan Adam.
Ainihin dalilin da ya sa ake samun rikici tsakanin wayewar kai, shi ne gazawar kallon sauran al’adu bisa wani matsayi na daidaiwa daida. Cikin dimbin shekarun da suka gabata, kasashen yamma sun dauki kansu tamkar cibiyar duniya, inda suka raba al’ummun duniya zuwa “masu ilimi wadanda ke da wayewar kai” da “wadanda ke cikin duhu”, yayin da suke kokarin gudanar da mulkin mallaka a wurare daban daban. Wannan ra’ayi na girman kai tushe ne ga akidar mulkin mallaka, wanda ya sa wasu kasashen yamma ke son yin babakere a duniya har zuwa wannan zamanin da muke ciki. Sai dai wannan ra’ayi na girman kai ya kan haifar da son zuciya da kiyayya da rikici da hargitsi a duniyarmu.
Wani misili game da tasirin girman kai na kasashen yamma shi ne matakan kafa shingayen ciniki da kasar Amurka ke son dauka. Cikin wani bayanin da Stephen Roach, shehun malami na jami’ar Yale ta kasar Amurka ya rubuta a kwanan baya, ya ce, dalilin da ya sa ake fama da matsalar gibin ciniki a Amurka din, shi ne manufar tattalin arziki ta kasar, wato samun gibin kudi sosai a kasafin kudin gwamnatin kasar, da karancin kudin da aka adana a bankunan kasar. Amma duk da haka, ’yan siyasar kasar na neman dora laifi kan kasar ta Sin, inda har suka kaddamar da matakan takaita shigar kayayyakin Sin cikin kasuwannin Amurka. Sai dai matakan sun mai da gibin cinikin da kasar Amurka ke samu kan kasar Sin, ya zama kan sauran kasashe, har ma gibin nan ya karu. Ta haka za mu iya ganin cewa, girman kai ne irin na kasashen yamma ya sa ’yan siyasar kasar Amurka son matsawa sauran kasashe lamba, da ta da rikici, maimakon yin kwaskwarima a cikin gida, yayin da suke neman daidaita matsalar da kasar ke fuskanta, duk da cewa matakin zai haifar musu da karin matsaloli.
A game da kasashen Afirka, ra’ayi mai kuskure a fannin wayewar kai na kasashen yamma shi ma zai iya zame musu shingayen hana ruwa gudu kan yunkurinsu na neman hanyar raya kai. A cewar wani shehun malami na kasar Uganda mai suna Nnanda Kizito Sseruwagi, wasu tunanin kasashen yamma sun shafi takamar da ake yi wai al’adun kasashen yamma sun fi na sauran kasashe, wadanda su kan haddasa rashin girmamawa da amincewa da tunani na musamman na al’ummun Afirka. Ban da haka, tunanin kasashen yamma ya kan bayyana huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasashen sauran yankuna a matsayin huldar takara da rikici da juna, lamarin da zai iya lalata huldar hadin kai, da hana cudanya da fahimtar juna, wanda sam ba zai amfani kasashen Afirka bisa yunkurinsu na samun ci gaba mai dorewa ba.
Sai dai ta yaya za a iya maye gurbin rikici da cudanya, a tsakanin mabambantan wayewar kai? To, ya kamata a yarda da matsayin daidaito a tsakaninsu, gami da yanayi na samun nau’ikan wayewar kai daban daban a duniyarmu, daga baya za a iya daidaita sabanin ra’ayi tsakanin mabambantan wayewar kai, da al’ummu, ta hanyar tattaunawa, da ingiza hadin gwiwa don amfanin juna. Ta hakan za a tabbatar da dabara mai dacewa ta kulla hulda tsakanin mabambantan wayewar kai, wadda za ta haifar da moriya ga daukacin dan Adam.
A cikin wani bayanin da ya rubuta, Nnanda Kizito Sseruwagi ya dauki huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin a matsayin wani misali, wajen shaida cewa cudanyar wayewar kai ta ingiza hadin gwiwa mai amfanawa juna. A cewarsa, wani babban dalilin da ya sa ake ta samun zurfafar hadin gwiwar Afirka da Sin, gami da samar da dimbin sakamako masu armashi, cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, shi ne domin kasashen Afirka da kasar Sin sun dade suna cudanya da juna, bisa matsayinsu na kasashe masu dadadden tarihi. Inda al’adunsu na gargajiya, da tunaninsu na bai daya, irinsu girmama tsoffi, da hakuri da bambanci, da neman samun jituwa tsakanin dan Adam da muhallin halittu, da dai makamantansu, suka zame musu tushen karfafa cudanya, da koyi da juna, gami da tabbatar da hadin kai mai dorewa.
Neman maye gurbin rikici da cudanya, a tsakanin wayewar kai daban daban, ra’ayi ne da kasar Sin ta dade tana tsayawa a kai, game da huldar wayewar kai da al’adun dan Adam. Wanda ya samu karbuwa da amincewa, daga dimbin kasashe masu tasowa. Wannan batu ya sa ake iya sa ran ganin wata makoma mai haske ta duniyarmu a nan gaba. (Bello Wang)