Ƙasar tsibirin Caribbean mai suna Curacao ta kafa tarihi, inda ta zama ƙaramar ƙasa a duniya da ta taɓa samun damar buga Gasar Cin Kofin Duniya, bayan ta tashi kunnen doki da Jamaica.
A baya, Iceland ce ke riƙe da wannan tarihi tun 2018, amma yanzu Curacao wadda mutanenta ba wuce mutane 150,000 kuma faɗin ƙasarta bai wuce mil 171 ba ta ƙwace wannan matsayi.
- Gwamnan Taraba Ya Dakatar Da Bikin Sauya Sheƙarsa Zuwa APC Saboda Sace Ɗaliban Kebbi
- Gwamnonin Arewa Sun Nemi A Gaggauta Ceto Ƴan Makaranta Mata Ta Kebbi Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Kocin Jamaica, Steve McClaren, ya yi murabus bayan ƙasar ta kasa samun nasarar da za ta kai ta gasar Kofin Duniya karo na farko tun 1998.
Sun yi iƙirarin samun bugun fenariti amma VAR ta soke.
A ɓangaren Curacao kuwa, kocinsu Dick Advocaat wanda bai halarci wasan ba saboda wasu dalilai, zai zama koci mafi tsufa a tarihin gasar Kofin Duniya da shekaru 78.
Ya karya tarihin Otto Rehhagel wanda ya je gasar da Girka yana da shekaru 71 a 2010.
Curacao, wacce ke kusan mil 37 daga gabar tekun Venezuela, ta zama ƙasa a masarautar Netherlands tun 2010 bayan rugujewar Netherlands Antilles.
A shekaru 10 da suka gabata ta kasance ƙasa ta 150 a jerin kasashen da FIFA ta fitar, amma yanzu ta dawo matsayi na 82.














