Aƙalla yara 10 ne suka rasu a Jihar Neja sakamakon ɓullar cutar diphtheria a ƙananan hukumomin Agaie da Bida.
An kai yaran da suka kamu da cutar asibitin Federal Medical Centre, Bida, amma sun rasu saboda matsalolin da cutar ta haddasa musu.
- Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
- “Hadin Kan Kasashen BRICS” Ya Karfafa Shawo Kan Kalubale
Mazauna wuraren sun nuna damuwa kuma suna roƙon gwamnati da ta hanzarta samar da rigakafi da magunguna don hana yaɗuwar cutar.
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Neja ta tabbatar da ɓullar cutar kuma ta ce an ƙaddamar da matakan gaggawa.
Hukumar ta ce tana samar da magunguna, sanya ido kan cutar, kuma tana buƙatar iyaye su tabbatar da cewa yaran su sun yi rigakafin diphtheria.
Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ke shafar maƙogwaro da hanyoyin numfashi, kuma tana iya hallaka mutum idan ba a yi saurin ɗaukar mataki ba.
Rigakafi shi ne babban mataki wajen hana yaɗuwar cutar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp