Daga Bello Hamza,
Shugaban kungiyar Likitoci reshen babbar birnin tarayya Abuja, Enema Amodu, ya bayyana cewa, Likitoci 20 ne suka mutu sakamakon kamuwa da suka yi da cutar korona a fadin kasar nan a cikin kwanaki 7.
Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a garin Abuja, ya ce, lallai ma’aikatan lafiya na tsanananin bukatar kayan kariya daga kamuwa daga cutar don kare rayuwarsu a yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Ya ce, dawowar cutar karo na biyu a fadin kasar na ya munana.
“Wannan dawowar cutar karo na biyu ya tsananta, musamman ganin mutane sun dauka cutar ta tafi, sun kuma koma yadda suke harkokinsu ada saboda haka cutar ta same su ba tare da sun shirya ba.
“Lamarin ya shafi bangaren harkar lafiya kwarai da gaske, don kuwa a cikin mako daya kawai mun yi asarar Likitoci fiye da 20 a fadin tarayyar kasar nan.”
Ya kuma kamata iyaye su zama masu gaskiya wajen hulda da likitoci ta yadda za a rage irin kasadar da likitocin ke fuskanta wajen yada cutar a gare su.
Ya kuma bukaci gwamnati ta kara alawus na Lilitoci, ya kuma yi kira ga al’umma Nijeriya su rungumi matakan kariya daga cutar a duk inda suka samu kansu don rage yadda cutar ke yaduwa.