Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum 42, sakamakon barkewar cutar kyanda a kananan hukumomin Mubi ta kudu da kuma Gombi a jihar Adamawa.
Kwamishinan ma’aikatar lafiya da ayyukan jinkai ga jama’a, Felix Tangwame, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar gwamnatin jihar a ranar Juma’a.
A cewar kwamishinan, cutar ta shafi unguwanni 8 a Mubi da kuma wasu unguwannin 7 a karamar hukumar Gombi, inda adadin wadanda suka mutu ya kai 42 daga cikin mutum 131 da kuma mutum 177.
Ya ci gaba da cewa “a bayanai rahoton bullar cutar, ma’aikatar lafiya ta dauki matakin gaggawa, da ya shawokan lamarin akan lokaci, har yanzu gwamnati da abokan huldarmu muna kan lura da sa’ido” inji Tangwame.
Ya kuma shawarci jama’a da su yi hattara da tsaftace muhalli, kuma a ko da yaushe su dauki matakan kariya daga kamuwa da cutar ta kyanda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp