Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye a jihohi 28 da kuma babban birnin tarayya, Abuja.
Alkaluman da ma’aikatar noma ta tarayya ta fitar a ranar Juma’a, sun nuna cewa sama da tsuntsaye miliyan daya ne abin ya shafa wanda da yawa suka mutu sannan da kiret din kwai 110,000 suka lalace.
- Sin Ta Yiwa Mambobin WHO Karin Bayani Kan Yanayin COVID-19 A Kasar
- “Sabon Ci Gaban Kasar Sin, Da Sabbin Damammaki Na Duniya” An Gudanar Da Zagayen Tattaunawa Na Turai-Asiya A Nan Birnin Beijing
Don haka ma’aikatar ta ce ana bukatar karin Naira biliyan 484 domin biyan diyya ga wadanda abun ya shafa.
“Don haka, gwamnati ta aiwatar da matakan kariya cikin gaggawa a jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Jigawa da Yobe,” in ji ta.
A cewar ma’aikatar, gwamnatin tarayya na duba yiwuwar yin allurar rigakafin cutar murar tsuntsayen a kowane lokaci.