Fannin kiwon Kajin gidan gona, na daya daga cikin fannin da ke saurin fadada, musamman duba da yadda fanin ke samar da ayyukan yi tare da samar wa wadanda suka rungume shi kudaden shiga da kuma rage yawan mazauna karkara da ke kwararowa zuwa cikin birane.
Don haka, ga wasu matakai biyar da mai kiwon Kajin gidan gona zai kaucewa yin asara:
1-Gina masu ingantaccen dakin kwana: Ana bukatar mai kiwon Kajin gidan gona ya tabatar ya gina musu ingantaccen dakin kwana, wanda hakan zai kare su daga kamuwa da sanyi, ana kuma so a rika sauya musu ruwan sha, domin gudun ka da su kamu da wasu cututtuka.
2- Ana so a tabbatar da muhallin da ake kiwonsu ya kansance tsaftace, don kaucewa bullar kwayoyin cutar da za su iya harbin su.
3- Ana so a rika duba yanayin lafiyarsu lokaci bayan lokaci:
Idan ana barin su suna shan ruwan kasa, za su iya harbuwa da kwayoyin cuta, musamman tsutsar ciki da za ta iya yi musu illa, sannan kuma duk irin yawan abincin da suka ci; ba za su yi wani nauyi ba, karshe ma za a ga suna ramewa.
Domin gujewa hakan, yana da kyau a rika duba lafiyarsu akai-akai, ta hanyar bin shawarwarin kwararrun masu kiwo.
4- Ana so a rika sanya musu haske a dakunan kwanansu:
Wannan zai ba su damar yin kwansu a cikin tsakani, musamman duba da cewa; suna da bukatar samun haske har na sa’oi 16, musamman don samun damar yin kwai masu yawan gaske.
5- Ciyar da su wadataccen abinci:
Ana bukatar a rika ciyar da su wadataccen abinci, yadda za su rika samun yawan dumi a jikinsu.
6- Yi musu inshora: Ana so a yi musu inshora don kaucewa yin asara duba da cewa, a lokacin damina sukan fuskanci wasu matsaloli ko cututtuka wadanda ke sa su rage yin kwai kamar yadda suka saba yi da yawa.
Wasu daga cikin cututukan da ke harbin Kajin gidan gona da damina:
a-Kurajen Kaji: Wannan wata babbar cuta ce da ke yi wa Kajin gidan gonar da suka harbu da ita illa. Akasari suna kamuwa da cutar ce, idan Sauro ya cije su da sauran kwarin da suka tsotsi Jinin jikinsu, wanda hakan na kashe su nan take.
Za a iya magance hakan ne, ta hanyar yi musu rigakafin kamuwa da cutar da kuma yi wa wajen kwanansu feshi.
b- Gudawa: Ita ma wannan cuta ce da ke yi wa Kajin gidan gonar da suka kamu da ita illa ga lafiyarsu, wadda har ma tana iya kai su ga halaka ko mutuwa. Akasari, ta fi harbin ‘yan Tsaki masu tsawon mako shida zuwa sama.
Cutar ta fi yaduwa a lokacin damina, idan sun kamu ba sa iya cin abinci; suna kuma yin numfashi ne da kyar da sauran makamantansu.
c- Zawo: Ita ma wannan cutar na harbin Kajin gidan gona daga kowane matakin girma nasu.
d- Cutar sanyi: Idan ana muku-mukun sanyi, suna fuskantar matsala; wanda take kaiwa ga ba sa jin dadin muhallin da ake kiwata su. Za a iya magance musu wannan matsalar kadai ta hanyar yin feshi a inda ake kiwon su.