Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki na kasa (DisCos) sun sanar da karin farashin wutar lantarki, wanda hakan ya zama karin farashin na biyu cikin watanni hudu.
Sabbin farashin, wanda zai fara aiki daga ranar Talata 5 ga watan Nuwamba, 2024, ya nuna yadda kowane kamfanin rarraba wutar na yankin kasar zai sayar da wutar kamar yadda Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta tabbatar.
- Kotu Ta Hana CBN Da Sauransu Yi Wa Kudaden Kananan Hukumomi Katsa-Landan
- Xi Ya Taya Boko Murnar Zabarsa A Matsayin Shugaban Botswana
A cewar DisCos, farashin mita mai hawa daya ya tashi daga kimanin naira 117,000 zuwa naira 149,800, ya danganta da kamfanin da ke raba wutar a yanki da kuma masu sayar da mitoci.
A jihar Kano, mita mai hawa daya, farashin yana tsakanin Naira 127,9925 zuwa Naira 129,999.75, sai kuma mita mai hawa Uku, tana tsakanin Naira 223,793 zuwa Naira 235,425.
A jihar Kaduna kuwa, mita mai hawa daya farashin yana tsakanin Naira 131,150 zuwa Naira 142,548.94 yayin da Mita mai hawa Uku ke tsakanin Naira 220,375 zuwa Naira 232,008.04.