Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta dakatar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da wasu sarakuna hudu da aka tsige a jihar daga bayyana kansu a matsayin sarakuna.
Hukuncin dai ya haramtawa Bayero tare da Sarakunan Bichi, Rano, Gaya, da Karaye, daga yin ikirari ko zartar da wani hukunci a matsayin sarakuna.
- Har Yanzu Tukunyar Rikicin Masarautar Kano Na Tafarfasa
- Kanana Hukumomin Kano Da Jigawa 23 Na Kan Gaba Wajen Fuskantar Ambaliyar Ruwa – NEMA
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a ranar 27 ga watan Mayun 2024 ne gwamnatin jihar Kano, ta bakin lauyanta, Ibrahim Isah-Wangida, ta nemi a dakatar da Bayero da sauran sarakunan hudu da aka tsige daga ikirari ko bayyana kansu a matsayin Sarakuna a Jihar.
Wadanda ake karar acikin shari’ar sun hada da Alhaji Aminu Ado Bayero (Sarkin Kano na 15), da Alhaji Nasiru Ado Bayero (Sarkin Bichi na biyu), da Dakta Ibrahim Abubakar II (Sarkin Karaye), da Alhaji Kabiru Muhammad-Inuwa (Sarkin Rano) da Aliyu Ibrahim-Gaya (Sarkin Gaya).
Sauran su ne sufeto janar na ‘yansanda, da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya a jihar (DSS), da hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC), da kuma rundunar sojojin Nijeriya.
Shari’ar dai ta biyo bayan dambarwar matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka ne na tsige sarakunan jihar guda biyar, wadanda tsohuwar gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta nada.
Matakin soke masarautun hudu daga cikin biyar din da gwamnatin baya ta kirkiro ya haifar da cece-kuce a jihar, inda Sarkin Kano na 15, Bayero ya ke zaman fada a karamar fadar Nasarawa da ke Kano yayin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka mayar ke zaman fada a babbar fadar gidan sarkin Kano.