A zamanta na yau Laraba ne Majalisar Dokokin jihar Adamawa ta amince da kudirin dokar da za ta soke da kuma sake kafa sabbin gundumomi ta jihar Adamawa, 2024.
Amincewar kudirin ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton zaunannen kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi da masarautu karkashin jagorancin Hon. Kefas Calvin (Mazabar Toungo).
- An Kashe ‘Yansanda 229 Cikin Watanni 22 A Nijeriya – Rahoto
- CBN Ya Raba Lambobin Da Za A Yi Karar Bankunan Da Ba Sa Saka Kudi A ATM
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Kate Raymond Mamuno (Mazabar Demsa) ta gabatar da kudirin yin karatu na 3 na kudirin kuma Hon. Suleiman Alkali na Yola ta Arewa.
Bayan kammala taron, shugaban majalisar Rt. Hon. Bathiya Wesley, ta umurci magatakarda da ya shirya tsaftataccen kwafin kudirin don amincewar Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.
Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne al’ummar jihar suka bukaci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ya samar da sabbin gundumomi, inda gwamnan ya mika bukatar ga majalisar dokokin jihar Adamawa domin amincewa.