‘Yan majalisar dokokin jihar Legas, a ranar Litinin, sun tsige kakakin majalisar, Rt. Hon. Mudashiru Obasa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin shugaban majalisar da almundahana da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma.
Ana zargin Obasa da kashe Naira biliyan 17 wajen saka wata kofar shiga harabar majalisar, wanda masu suka suka ce ya wuce gona da iri kuma akwai zamba aciki.
Ana kuma zarginsa da karkatar da kudaden ayyukan mazabu.
Cikakkun bayanai Daga baya…