Wata tankar mai ta fashe kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane 30 a hanyar Agaie-Bida a jihar Neja da safiyar Lahadi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, tankar ta yi karo ne da wata tirela dauke da shanu wacce ta nufi jihar Legas daga Wudil a jihar Kano.
Babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Mallam Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Cikakken bayanai na tafe…