Majalisar zartarwa a fadar gwamnatin tarayya ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga yankin Arewa ta tsakiya a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Shugaba Bola Tinubu ne ya gabatar da Amupitan a matsayin wanda zai cike gurbin shugabancin hukumar bayan ficewar Farfesa Mahmood Yakubu. Yakubu ya jagoranci INEC ne daga 2015 zuwa Oktoban 2025.
- Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
- Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, shugaba Tinubu ya shaidawa majalisar cewa, Amupitan shi ne mutum na farko da ya fito daga jihar Kogi ta arewa ta tsakiya da aka zaɓa domin ya cike gurbin kuma ba ɗan siyasa ba ne.
‘Yan majalisar dai sun amince da naɗin, inda Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya.
Dangane da kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara), yanzu Shugaba Tinubu zai aika da sunan Amupitan zuwa Majalisar Dattawa don tantancewa.
Amupitan, mai shekaru 58, daga Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Farfesa ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, Filato, kuma tsohon ɗalibin jami’ar ne.