Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin cigaba da karbar tsofaffin takardun kudi na N200 zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2023.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka fitar aka watsa a kafafen sadarwa na kasar a ranar Alhamis.
“Ina yi muku jawabi a matsayin zababben shugaban kasa bisa tafarkin dimokuradiyya domin jajanta muku kan wahalhalun da ake fuskanta sakamakon tsarin sauya fasalin Naira.”
“Don kara saukaka wa ‘yan kasarmu kan matsalolin da tsarin sauya fasalin kudin ya haifar, na amincewa CBN sake fitar da tsofaffin takardun kudi na N200 su cigaba da zagayawa tare da sabbin takardun kudin N200, N500, da kuma N1000 na tsawon kwanaki 60 daga 10 ga Fabrairu, 2023 zuwa 10 ga Afrilu, 2023 lokacin da tsohuwar takardar N200 ita kuma ta daina aiki.”
‘Yan Nijeriya dai na fama da karancin sabbin takardun kudi na Naira, lamarin da ya haifar da dogon layi a dakunan bankuna, da na’ura mai sarrafa kudi (ATM).
An dai gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar sakamakon karancin sabbin takardun kudi na Naira.