Manir Muhammad Dan’iya mataimakin gwamnan jihar Sakkwato ya fice daga jam’iyyar PDP.
Dan’iya ya mika takardar murabus dinsa ne a wata takarda da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Kware da ke karamar hukumar Kware a jihar Sakkwato.
Wani bangare na Wasikar kamar haka: “Na rubuta wannan takarda ne domin in sanar da ku ficewata daga jam’iyyar PDP daga ranar 8 ga watan Fabrairun 2023.
“Na yaba da damar da aka ba ni, wanda ya sa na yi aiki a wurare daban-daban a karkashin PDP,”.
Duk da cewa Dan’iya bai bayyana jam’iyyar da ya koma ba, amma majiyoyi sun ce yana kan hanyarsa ta koma wa jam’iyyar APC.
Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa “zai iya sauya sheka zuwa APC a yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi a Sakkwato a yau.”
Hakan dai ba zai yiwa jam’iyyar PDP dadi ba ganin cewa kwanaki 16 ya rage a yi zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Mataimakin gwamnan shine dan takarar sanata na jam’iyyar PDP a shiyyar Arewacin Sakkwato.
Gwamna Aminu Tambuwal shi ne Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023.