A daren jiya ne zuwa wayewar garin yau Asabar gungun ɗan ta’addan da ya addabi yankin Masarautar Ɗan Sadau, mai suna Damuna, suka sace fiye da mutum 150 inda suka kora su cikin daji.
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Mutunji, Kwanar Dutsi, Sabon Garin Mahuta da Unguwar Kawo.
‘Yan ta’addan sun yi wa ƙauyukan ƙawanya tare da awon gaba da maza da mata da kananan yara fiye da 150 saboda sun ki biyan kudin fansa na aikin gona Naira Miliyan 120 da aka sanya masu tun kafin fara aikin kaka.
Wani mazaunagrin Kwanar Dutsi, Jamo Maude ya bayyana ma wakilin mu cewa, jigon ‘yan ta’addan Damuna, ya kai harin ne a kauyukan da babura sama da 100 ɗauke da mutane biyu-biyu da muggan makamai inda suka kora mutanan zuwa cikin daji a cikin daren na jiya Juma’a.
Ya zuwa yanzu ba asan halin da mutanan ke cikin ba.
Wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yansandan Jihar Zamfara ,SP Yazi Abubakar ta waya amma wayar ta ki shiga,ballantana a ji ta bakinsa. Amma dai yana ci gaba da nema.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp