Kwanan nan, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta bayyana cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya bayan nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya game da batun haraji ba.
Wannan batu dai martani ne ga wasu rahotanni daga bangaren Amurka dake cewa, yana tattaunawa da bangaren Sin dangane da batun haraji. Tun da farko, Sin ta yi gargadi tare da jan kunne cewa, yakin cinikayya ko na haraji, ba zai haifar da da mai ido ba, haka kuma, babu wanda zai ci nasara. Amma Amurka ta yi biris, ta kuma yi gaban kanta wajen sanya haraje-haraje marasa kan gado tare da jefa duniya cikin rudani.
- Rashin tsaro: Gwamnan AbdulRahman Ya Gana Da Sarakuna Masu Daraja Ta Daya A Jihar Kwara
- Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Sabbin Hadimai 173
Shin Amurka tana kokarin neman sulhu ne? Da alamu ta fara dandana kudarta duba da yadda ta fara irin wadannan kalamai. Kuma ko a baya bayan nan yayin wani taro da masu zuba jari, sakataren Baitul-malin kasar Scott Bessent ya shaida musu cewa nan ba da dadewa ba, za a shawo kan tankiyar ta haraji dake tsakanin bangarorin biyu.
Kamar yadda Sin da masana suka sha fada, mummunan matakin na Amurka, zai fi yi mata illa maimakon kasashen da take neman cin zalinsu.
Tabbas Sin ta yi gaskiya da ta ce bayar da kai ko ja da baya, dama ce ga mai cin zali. Don haka, Sin ta yi daidai da ta tsaya haikan wajen mayar da martani ba tare da bada kai ba, domin Amurka ta gane kuskurenta, kana ta fahimci cewa, lokaci ya wuce da za a rika biye mata tana yin abun da ta ga dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp