Tun a ranar 24 ga wannan wata ne, kasar Japan ta fara sakin ruwan dagwalon tashar nukiliyar Fukushima zuwa cikin teku, lamarin da ya gamu da rashin amincewa daga bangarori da dama daga ciki da wajen kasar. Sanin kowa ne cewa, batun amincewa da shirin Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku, ba batu ne da wasu kasashe tsiraru za su amincewa ba, musamman karkashin bukatun kasashe na cimma burin siyasa.
A shekarar 2021 ne dai Japan ta bijiro da wannan aniya, bayan da wata girgizar kasar ranar 11 ga watan Maris din a shekarar 2011 da ta lalata tashar nukiliyar Fukushima, tare da haddasa yoyon sinadarin nukiliya, tun lokacin ne kuma aka rika nusar da Japan da ma wadanda suka bayar da shawarar aikata wannan danyen aiki.
Idan ba a manta ba, shi ma taron kasashen nan 7 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7 da ya gudana a kasar ta Japan, bai goyi bayan shirin kasar na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku ba, saboda illarsa ga yanayin teku da tsaron abinci da ma lafiyar daukacin bil-Adama, amma bangaren Japan ya ci gaba da yin kunnen uwar shegu da neman kare kansa ta kowace hanya, wai don saboda arahar wannan tsari, wanda masu iya magana ke cewa, ba ta ado.
Abin takaici shi ne, yadda Japan ta dage cewa, wai shirin nata ya samu amincewar Amurka, da wasu karin kasashen ma yaudarar kai ne kawai, saboda wannan danyen aiki zai shafi lafiyar al’ummar duniya ne baki daya.
Ya kamata Japan ta fahimci cewa, akwai kasashe kusan 200 a duniya, kuma kalilan ne suka bayyana amincewa da shirin nata. Hasali ma dai mafi yawan kasashen duniya ciki har da al’ummar Japan da kansu, sun bayyana adawa, da rashin gamsuwa da zubar da ruwan dagwalon nukiliyar cikin teku.
Gaskiyar al’amari shi ne bai kamata Japan ta kawar da kai daga gaskiya ba, balle kuma ta rika yaudarar kanta”. Wannan ya kara nuna cewa, Japan ba ta damu da lafiyar jama’arta ba, balle ma ta damu da lafiyar al’ummar duniya. Abin dake tabbatar da cewa, Japan ta debo ruwan dafa kanta da kanta.
Yanzu dai kasar Sin ta dauki matakin kare lafiyar jama’arta da ma na ragowar kasashen duniya, ta hanyar haramta shigo da kayan ruwa daga Japan, tun lokacin da Japan din ta fara sakin ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku.
Masharhanta na cewa, zubar da ruwan dagwalon nukiliyar da Japan ta yi, ko shakka babu zai shafi muhallin teku da lafiyar bil adama. Kuma mataki ne na nuna karfin iko, da yin watsi da damuwar sassan kasa da kasa, da martaba moriyar kai, da yin fatali da moriyar sauran sassan kasa da kasa. Amma kowa ya debo da zafi aka ce bakinsa.
Sai dai a maimakon gyara kuskuren da ya yi, bangaren Japan ya rika nuna yatsa ga kasar Sin. Kafofin yada labaran kasar Japan da dama sun yi ta yayata zargin da ake yi na cewa, kiyayyar Japanawa a kasar Sin na kara zafafa, kuma Sinawa na daukar matakan “tsana” kan kasar Japan. Firaministan Japan Fumio Kishida da wasu ‘yan siyasar kasar da dama, sun bukaci kasar Sin da ta soke takunkumin hana shigo da kayayyakin ruwa na Japan, har ma sun yi barazanar daukar matakai kan wannan lamari.
Wannan wani bangare ne na yakin “ra’ayin jama’a” da Japan ta shirya a hankali. A ranar da Japan din ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, a cewar kafar watsa labarai ta kasar Japan NHK, ma’aikatar harkokin wajen Japan ta tsara manufar daidaita abin da aka kira “labaran karya”, yawan kudin da ta ware domin aiwatar da manufar ya kai kusan JPY biliyan 70. Idan aka duba rahoton daidaita ruwan dagwalon nukiliya da Japan ta fitar a shekarar 2020, yawan kudin da Japan ta ware wajen daidaita labaran karya, ya fi kasafin kudin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku yawa har sau 20.
Ana iya ganin cewa, bangaren Japan ya zabi zubar da ruwan dagwalon nukiliya zuwa teku don tsimin kudi, amma ya kashe kudi da yawa don kawata shi. An yi nuni da cewa, bangaren Japan yana zargin Sin yana dora wa kasar Sin laifi ne, domin rikitar da ra’ayin jama’a da kuma mayar da kanta a matsayin “wadda aka raunata”, ta boye abin da ta yi na gurbata muhalli da kuma illata lafiyar bil Adama, a yunkurin rage zargin da ake yi mata dangane da batun zubar da ruwan dagwalon nukiliya zuwa teku. (Ibrahim Yaya, Safiyah Ma)