Biyo bayan matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na mika al’amuran jam’iyyar APC ga tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, jaridar PoliticsDigest ta rahoto cewa, Ganduje ya mika sunan tsohon mataimakin gwamnan Kano Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ga shugaba Tinubu a matsayin wanda zai maye gurbinsa a mukamin Minista.Â
An fahimci cewa tun farko, Ganduje ya so mika sunan tsohon sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji a matsayin wanda zai maye gurbinsa amma ya sauya shi da Abdullahi Gwarzo sabida kusancinsa da shugaba Tinubu.
Babu tabbas ko sunan tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar NNPP yana cikin jerin karin sunayen ministocin Tinubu.
A baya dai, an yi hasashen cewa Kwankwaso da wani daga Kano na cikin jerin karin sunayen ministocin Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp