Zababben Sanatan Akwa Ibom ta Kudu-maso-Yamma, Godswill Akpabio, ya doke zababben Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdul’aziz Yari, a zaben Shugaban Majalisar Dattawa ta 10 da aka yi a safiyar ranar Talata.
Akpabio ya samu kuri’u mafi yawa daga cikin kuri’u 109 da aka kada.
Sanata Godswill Akpabio, ya samu kuri’u 63 inda ya doke Abdulaziz Yari daga Jihar Zamfara wanda ya samu kuri’u 46.
Cikakken bayani na tafe….
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp