An harbi tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, a gabashin kasar ranar Alhamis, lamarin da ya kai shi ga jin mummunan rauni, kamar yadda hadiminsa ya bayyana.
An kai harin ne a yankin Wazirabad mai tazarar kilomita 200 daga Islamabad babban birnin kasar.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matar Kwamandan NSCDC A Jihar Nasarawa
- Ma’aikatan N-Power Sun Yi Zanga-Zangar Kin Biyansu Hakkokinsu A Bauchi
A cewar wani memba na jam’iyyar Khan ta Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI), da yawa daga cikin abokan aikin Khan sun samu raunuka.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa mutum daya ya mutu.
“Wani mutum ne ya bude wuta da bindiga. Mutane da dama sun jikkata. Imran Khan ma ya samu rauni,” Asad Umar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Khan, wanda tsohon dan wasan Cricket ne, ya jagoranci wata zanga-zanga a Islamabad don neman a gudanar da zabe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp