Ayau ranar Alhamis ce 25 ga Augustan 2022, aka Kammala tsara rukunin kungiyoyin kwallon kafa na turai da zasu gwabza a gasar cin Kofin Turai na Shekarar 2023.
Kungiyar Bayern Munich, Barcelona da Inter an hada su cikin ‘Rukuni mawuyaci’ yayin da kungiyar Manchester City da Liverpool suka afka cikin hali mai matsakaicin tangarda.
Chelsea da Tottenham sun samu sauki sosai, yayin da PSG da Juventus za su fafata a zagayen farko a gasar.
- Rukunin A: Ajax, Liverpool, Napoli, Rangers
- Rukunin B: Porto, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Club Brugge
- Rukunin C: Bayern Munich, Barcelona, Inter, Viktoria Plzen
- Rukunin D: Eintracht Frankfurt, Tottenham Hotspur, Sporting CP, Marseille
- Rukunin E: AC Milan, Chelsea, FC Salzburg, Dinamo Zagreb
- Rukunin F: Real Madrid, RB Leipzig, Shakhtar Donetsk, Celtic
- Rukunin G: Manchester City, Sevilla, Borussia Dortmund, Kobenhavn
Rukunin H: PSG, Juventus, Benfica, Maccabi Haifa