Daga karshe dai farashin man fetur ya tashi daga Naira 165 da ake sayarwa kan kowace lita a sassan kasar nan.
Duk da cewa an jima ana siyar da man fetur din akan sama da Naira 165 a wasu sassan kasar nan, amma an fitar da sabon tsarin farashin a ranar Talata.
- ‘Yan Sanda Sun Yi Ram Da Mahalarta Bikin Auren Jinsi A Katsina
- ‘An Kashe Mayakan Boko Haram Da Yawa A Wani Hari Da Sojoji Suka Dakile A Neja’
‘Yan kasuwar man fetur sun ce Gwamnatin Tarayya ta amince da karin kudin, amma har yanzu Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ba ta mayar da martani kan hakan ba.
An yi kokarin samun tabbaci daga NMDPRA a safiyar ranar Talata amma kakakin hukumar, Mista Apollo Kimchi bai ce komai kan lamarin ba.
Dangane da karin sabon farashin da aka fitar a ranar Talata, farashin ya tashi daga N165 zuwa N179 kowace lita a kudu maso yamma, kudu maso kudu da kudu maso gabas.
An kara farashin zuwa N184 a arewa maso yamma da kuma N189 a arewa maso gabas wanda aka samu karin N24, a sabon farashin.
Yanzu dai za ake sayar da man fetur a kan N179 a yankin arewa ta tsakiya, sai dai za ake sayar da shi kan N169 a Legas, ‘yan kasuwa za su sayar da shi a kan N174 a Abuja.
Haka kuma an samu daidaiton farashin tsohon a Legas daga N148.17 zuwa N160 da 162.