• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

DA DUMI-DUMI: An Sace Mutum 16 A Wani Sabon Hari Da Aka Kai Jihar Kaduna

byMuhammad
3 years ago
Da

A wani sabon hari da ‘Yan bindiga suka kai sun sace mutane 16 a unguwar Angwan Pa da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce maharan sun afkawa yankin a ranar Litinin da misalin karfe 7:30 na dare, sa’o’i 24 bayan harin ranar Kirsimeti da aka kai Angwan Aku, da ke karamar hukumar Kajuru, inda aka kashe mutum 1 tare da jikkata wasu da sace mutum 45.

  • Wani Shahararren Dan Bindiga Ya Shiga Hannun ‘Yansanda A Jihar Kaduna
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 37 Tare Da Kone Gidaje Sama Da 100 A Garin Kaura, Kaduna

Mazaunin yankin wanda ya bukacu a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun mamaye yankin ne da misalin karfe 7:30 na dare inda suka kewaye kauyen, suka yi ta yin harbe-harbe.

Ya ce yayin kai harin sun yi awon gaba da mutane 53 amma 37 daga cikinsu sun tsere inda suka koma gida a safiyar ranar Talata, inda suka yi garkuwa da 16.

A cewarsa, kananan kauyukan da ba su da yawa a yanzu ‘yan bindigar ne ke kai hari, yana mai jaddada cewa: “Ba mu yi tsammanin ‘yan bindigar za su kai wa Anguwan Pa hari ba, domin bayan harin da aka kai wa Anguwan Aku a ranar Lahadin da ta gabata, an tura sojoji domin kwantar da tarzoma a yankin.

LABARAI MASU NASABA

Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

“’Yan bindigar sun zo ne da misalin karfe 7:30 na yammacin jiya ramar Litinin inda suka kewaye kauyen. Yawancin lokaci suna zuwa da yawa sosai dauke da makamai.

“Za su shiga cikin yankin kawai, kafin ku ankara, sun riga sun kewaye ko’ina.

“Idan ka gudu za su harbe ka su kashe ka. Ba su saba shiga manyan yankuna da ke da yawan jama’a ba.

“Suna kai hari kananan kauyukan da ba su da mutane da yawa. Ba sa kuskura su shiga manyan kauyuka domin su ma suna tsoron asarar rayukansu.

“Yawancin mutanen karkara a Kajuru suna rayuwa ne cikin tsoro da fargaba.” A cewarsa.

An tuntubi, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, don jin halin da ake ciki kan sabon harin sai dai bamu samu amsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi
Da ɗumi-ɗuminsa

Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

October 1, 2025
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
Da ɗumi-ɗuminsa

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

September 17, 2025
DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
Da ɗumi-ɗuminsa

DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu

September 16, 2025
Next Post
Ana Gab Da Kammala Ginin Hedkwatar Africa CDC Da Sin Ta Dauki Nauyinsa

Dangantakar Sin Da Afrika Ta Kai Wani Mataki Da Babu Wanda Zai Iya Lalatawa

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version