Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta sanar da cewa an yi mata kutse shafinta na yanar gizo.
A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a daren Laraba, hukumar ta ce tana aiki don dawo da shafin.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Tabbaci Ga Duniya
- Tinubu Ya Isa Legas Don Gudanar Da Bukukuwan Kirsimeti Da Sabuwar ShekaraÂ
Ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da duk wani saÆ™o ko rahoto da aka gani a shafin har sai an gyara shi.
A halin yanzu, saÆ™on gargadi ne a shafin “An Yi Kutse A Shafinmu”, kuma ba za a iya ci gaba da ziyartar shafin ba.
Hukumar Kididdiga ta Kasa, ita ce ke da alhakin samar da kididdiga a hukumance a Nijeriya.