Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta cimma yarjejeniya da Tottenham wajen sayan dan wasan gaba na kungiyar Harry Kane, a kan kudi €100 kamar yadda jaridar The Athletic ta ruwaito.
Tun a watan da ya gabata Tottenham tayi fatali da tayin kudi har sau uku da Bayern Munchen take kaiwa domin siyan dan wasan mai shekara 30 a duniya.
Kane, ya bayyana cewa yana son sanin makomar sa kafin kungiyar ta Tottenham ta buga wasan ta na farko a gasar premier league ta Ingila.
Yanzu Bayern Munchen tana jiran amincewar dan wasa Kane domin ci gaba da kammala cinikin.
Tun bayan da dan wasa Robert Lewandowski ya bar Bayern Munchen ya koma Barcelona kungiyar bata sayi babban dan wasan gaba ba.