A karshe dai, babban bankin Nijeriya CBN ya magantu kan hukuncin da kotun koli ta yanke kan cigaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da kuma N1000 har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.
Mukaddashin daraktan sadarwa na CBN, Isa Abdulmumin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin.
“A bisa bin umarnin kotu da bin doka da oda da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi, da kuma matsayin Babban Bankin Nijeriya (CBN) mai kula da shige da ficen kudaden kasa. Ya umurci bankunan da ke aiki a Nijeriya da su bi hukuncin da kotun koli ta yanke na ranar 3 ga Maris, 2023,” in ji sanarwar.
“Sabida haka, CBN ya gana da kwamitin ma’aikatan banki kuma ya ba da umarnin cewa tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 su ci gaba da zama a matsayin halastaccun kudi tare da sabbin kudin da aka sauyawa fasali har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.” Inji shi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp