Hukumar kula da dazuka da yankunan ciyayi ta kasar Sin, ta ce fadin yankin dazukan kasar Sin ya karu da kadada miliyan 22 cikin shekaru 10 da suka gabata.
Wannan kari da aka samu, ya taimaka sosai wajen inganta muhallin halittu a kasar, haka kuma ya bayar da gudunmuwar kaso 1 bisa 4 na sabbin dazuka na duniya.
Yanzu fadin dazuka a kasar ya tsaya kan kimanin kaso 24.02 bisa dari, karuwar kaso 8.6 kan na shekarar 1949, lokacin da aka kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Talla