Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya karyata labaran da ke yawo da kafafen yada labarai cewa wata majiya ta tsugunta musu cewa bankin ya umarci bankunan kasuwanci da su cigaba da karbar tsofaffin takardar kudin N500 da N1000.
A wata sanarwar da CBN ya fitar, a yammacin ranar Juma’a, ya misalta batun da cewa na karya kuma babu gaskiya a cikinsa.
Kakakin CBN, Osita Nwanisobi, ya ce, babban bankin na nan daram kan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar, na cewa zallar takardar tsohuwar takardar Naira 200 ne kawai aka amince ya ci gaba da amfani har tsawon kwanaki 60 kacal.
“Hankalin Babban Bankin Nijeriya ya karkata kan wasu labarai na karya da ke cewa CBN ya amince wa bankuna su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudin 500 da 1000.
“Domin kauce wa shakku ko kokwanto, CBN na bin umarnin da shugababn kasa Muhammadu Buhari ya bayar na cewa a sake bada damar amfani takardar kudin 200 ta sake yaduwa cikin al’umma tare da sabon wanda aka yi har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.
“Saboda haka muna shawartar al’umma da su yi watsi da wannan batun domin ba daga CBN bayanin ya fita ba.”
Daga nan kuma sanarwar ta bukaci ‘yan jarida da suke tabbatar da sahihancin labari ko bibiyar madogarsu kafin yadawa ga jama’a don gudun jefa jama’a cikin shakku.