Chelsea na neman sabon kocin da zai maye gurbin kocinta a wani lamari kamar almara, sallamar kocin da ya lashe gasar zakarun Turai Thomas Tuchel a kungiyar.
Chelsea ta sallami Thomas Tuchel bayan rashin nasara da Dinamo Zagreb 1-0 ranar Talata a gasar zakarun Turai.
An nada Thomas ne a matsayin magajin tsohon dan wasan kungiyar Frank Lampard a watan Janairun 2021 kuma ya jagoranci Chelsea zuwa gasar zakarun Turai inda yayi nasara da ci 1-0 a kan Manchester City a watan Mayu na shekarar.
Daga nan, Tuchel ya samu nasarori da dama ta hanyar lashe kofuna a gasar cin kofin UEFA Super Cup da kuma gasar cin kofin duniya na kungiyoyi, amma Tuchel ya kuma yi rashin nasara a gasar cin kofin FA guda biyu da kuma wasan karshe na gasar cin kofin EFL – wanda aka doke shi a wasannin cin kofin gida biyu a bugun fanareti da Liverpool a bara.
Hukuncin da gwamnatin Birtaniya ta yi wa tsohon mai kungiyar, Roman Abramovich a lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine, ya haifar da tilasta wa Roman sayar da Chelsea zuwa LA Dodgers Todd Boehly akan Kudi yuro biliyan £4.25bn.
Chelsea ta taka rawar gani a kasuwar siyan ‘yan wasa a Wannan Shekarar, inda ta kawo ‘yan wasa irin su Raheem Sterling, Pierre-Emerick Aubameyang, Wesley Fofana, Kalidou Koulibaly da Marc Cucurella.
Blues dai ta fara gasar wasar bana da kafar hagu, duk da cewa ta yi nasara a wasanni uku, ta yi rashin nasara a wasanni biyu sannan ta yi kunnan doki da daya a cikin wasanninta na farko na gasar Premier shida, inda ta zama ta shida a kan teburi.
Rashin nasarar da Chelsea tayi a wasanta da kungiyar Dinamo a ranar Talata ya fusata sabbin masu kungiyar din suka kawo karshen kwantiragin Tuchel da kungiyar.