An zabi tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Ya gaji Sanata Abdullahi Adamu, wanda ya yi murabus bisa wasu rigingimu a watan jiya.
- Shugabancin APC: NEC Za Ta Bayyana Matsayar Ganduje A Yau
- Fitaccen Malamin Musulunci Dokta Ismail Surty, Ya Rasu A Birtaniya
An zabi Ganduje ne a taron kwamitin zartaswa na kasa karo na 12 da aka gudanar a Abuja.
Leadership Hausa ta ruwaito yadda Shugaba Bola Tinubu ya nuna sha’awar Ganduje ya gaji Adamu.
An kuma tabbatar da tsohon kakakin majalisar dattawa, Ajibola Bashiru a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa.
Baya ga Tinubu, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyar da dama sun halarci taron na NEC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp