Gobarar ta kone kayayyakin amfani da kadarori na miliyoyin Naira yayin a gobarar da ta tashi a safiyar ranar Litinin.
Gobarar ta ci shaguna da dama, lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa da mazauna yankin cikin damuwa da firgici sakamakon asarar da aka tabka a kasuwar.
- Gwamnatin Kogi Na Tuhumar Sarki Kan Zargin Bangaranci A Siyasa
- Yahaya Bello Ya Kulle Asusun Gwamnatin Kogi
LEADERSHIP ta rawaito cewa, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5 na safe inda cikin kankanin lokaci ta bazu cikin manyan shagunan kasuwar.
Muyane da dama da suka je wurin sun yi kokarin kashe gobarar da hana ta ci gaba da yaduwa, amma duk da kokarin da suka yi sun gaza kashe wutar.
Wasu da lamarin ya faru kan idonsu sun ce, masu shagunan ba su tsira da komai na kayansu don a kan idonsu suna kallon kayansu na ci da wuta.
Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar, sai dai mutanen yankin na Kabba sun nuna rashin damuwarsu kan rashin kayan aikin kashe gobara a kasuwar da zai taimaka wajen kashe wutar a kan lokaci.