Kotun shari’ar Muslunci da ke Filin Hoki a Jihar Kano, karkashin jagoranci mai Shari’a Abdullahi Halliru ta aike da ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.
Lauya Lamido Abba Soron Dinki, ya karanto mata tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Raba Auren ‘Yar Ganduje Da Mijinta
- Ka Mutunta Girmanka, Ka Janyewa Kwankwaso — Martanin NNPP Ga Atiku
Ana zargin Murja da bata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokan juna ne.
Kotun ta dage sauraren karar zuwa 16 ga watan Fabrairu, 2023.
Sai dai lauyan Murja, Barista Yasir Musa, ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun ba ta amince ba.
Idan ba a manta ba jami’an tsaro sun cafke Murja a satin da ya wuce, inda suka tuhumeta da bata tarbiyyar yara da kuma yin zage-zage da rawar fitsara a kafofin sada zumunta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp