Babbar kotun jiha da ke zamanta a Akure, babbar birnin Jihar Ondo, ta kori mataimakin kakakin Majalisar Dokokin jihar, Hon. Samuel Aderoboye.
Alkalin kotun, mai shari’a Adetan Osadebey, ta kuma umarci a dawo da tsohon mataimakin kakakin majalisar, Ogundeji Iroju.
- Tsohon Minista Ya Maka Gwamnatin Bauchi A Kotu Kan Tsigeshi A Wazirin Bauchi
- Mun Biya Biliyan 173.2 Kudin Daidaita Farashin Man Fetur Cikin Shekara 4 – Gwamnati
Kotun ta ayyana cewa cire Iroju a matsayin matakin Kakakin Majalisar da wasu mambobin Majalisar suka yi a ranar 24 ga watan Nuwamba 2020 an yi ne ba bisa ka’ida Kuma haramtaccen cirewa ne.
Shi dai Ogundeji an tsige shi ne a matsayin mataimakin Kakakin a 2020 bayan rashin jituwar da suka samu da Kakakin Majalisar Rt. Hon. David Oleyeloogun, kan yunkurin tsige mataimakin gwamnan Jihar, Hon. Agboola Ajayi.
Bisa rashin gamsuwa da cire shi, Iroju ta hannun lauyansa Mr. Wale Omotoso, SAN, sun garzaya kotun tare da cewa ba a bi matakan da suka dace ba wajen cire shi.
A hukuncinta a ranar Laraba, Mai Shari’a Osadebey ta ce, kwamitin da Majalisar ta kafa bai wa dan majalisar ‘yancin ji daga gareshi ba kafin cireshi. Kana kuma ba a bi dokoki ba wajen aiwatar da hakan.
Kotun ta umarci a dawo da Iroju ofishinsa kuma dukkanin wasu hakkoki tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu a biyanshi.
Justice Osadebey ta kuma umarci a biya shi naira miliyan 10 a matsayin ma bata masa ta hanyar cireshi da dakatar da shi.