Tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Alhaji Muhammad Bello Kirfi, ya maka gwamnatin Jihar Bauchi a kotu kan kalubalantar tsige Wazirin Masarautar Bauchi.
LEADERSHIP Hausa ta nakakto cewa, Alhaji Bello Kirfi wanda tsohon minista ne a zamanin mulkin Alhaji Shehu Shagari da zama ministan ayyuka a zamanin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo an ciresa a matsayin Wazirin ne bisa zarginsa da rashin da’a da biyayya wa gwamna Bala Muhammad a ranar 3 ga watan Janairun 2023.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 4 A Anambra
- Tinubu Ne Kadai Zai Iya Magance Rashin Tsaro Da Tabarbarewar Tattalin Arziki – Buhari
Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun Bello Kirfin, Barista Yakubu Bello Kirfi ya fitar a ranar Laraba, ya musanta labaran da wasu kafafe suka yada da ke cewa zai yi duk abun da zai iya yi wajen tabbatar da Bala Muhammad bai samu nasarar zarcewa ba a zaben 2023. Ya misalta labaran da cewa babu gaskiya a cikinsu.
Bello Kirfi ya nuna cewa a matsayinsa na musulmi mai imani da ya yarda iko na hannun Allah, kuma shi ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so ya amsa daga hannun wanda ya so a lokacin da ya so, “Cire Alhaji Muhammad Bello Kirfi da gwamnatin jihar Bauchi ta yi ta hanyar amfani da masarauta ya janyo cece-kuce a jihar.
“Mutane da dama sun zo domin jajantawa da nuna alhininsu tare da nuna goyon baya kan wannan lamarin. Muna godiya musu.”
Ya ce, sun tafi kotu domin neman hakki kan cire Bello Kirfi a matsayin Waziri, “Lamarin ma a halin yanzu na gaban kotu.”