Kotu ta yanke wa dan takarar gwamna a jam’iyyar YPP, Bassey Albert hukuncin daurin shekaru 42 a gidan yari, bayan samunsa da laifin cin hanci da rashawa.
Kotun da ke zamant a Jihar Oyo, ta zartar wa da dan takarar gwamnan hukuncin ne biyo bayan gurfanar da shi da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kasa (EFCC) ta yi a gaban kotun.
- Kungiyar Mata ‘Yan Jarida Ta Yi Sabuwar Shugaba A Kebbi
- Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Takaicin Yadda Gwamnoni Ke Mayar Da Kauyuka Saniyar Ware
Tuni aka tisa keyarsa zuwa gidan yarin Ikot Ekpene da ke Jihar Akwa Ibom, don fara zaman wakafinsa.
Mista Albert wanda Sanata ne mai wakiltar mazabar Akwa Ibom ta Arewa Maso Gabas, an same shi da karbar cin hancin motoci 13 da kudinsu ya kai darajar Naira 254 daga hannun wani dan kasuwar man fetur mai suna Olajidee Omokore daga 2010 zuwa 2014.
Sanatan yana jam’iyyar PDP lokacin da lamarin ya faru, amma a daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar YPP, inda ya samu tikitin tsayawa takarar gwamnan jihar.
Zai kara da dan takarar jam’iyyar PDP, Umo Uno a zaben 2023, mai karatowa.