Majalisar Dattawa ta amince da kudirin bai wa dalibai rance a matsayin doka, biyo bayan tsallake karatu na uku da kudirin ya yi a ranar Laraba.
Wannan na zuwa ne biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin majalisar mai kula da manyan makarantu, wanda shugaban kwamitin, Sanata Muntari Dandutse, ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.
- Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2
- Gwamnatin Tarayya Ta Gano Mutane 9, ‘Yan Canjin Kudi 6 Masu Tallafawa Ta’addanci A Nijeriya
Idan za a tuna a makon da ya wuce ne, kudirin ya tsallake matakin karatu na biyu a zauren majalisar.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar dattawa da ta wakilai wasikar kan bukatar soke shirin bai wa dalibai bashi.
Sabuwar dokar za ta inganta tsarin bayar da lamunin manyan makarantu, domin magance matsalolin dalibai da suka shafi daina zuwa makaranta, hanyoyin samun kudi da kuma hanyoyin biyan lamunin.
Matakin na Tinubu ya biyo bayan sanarwar dakatar da fara shirin bai wa dalibai rance na wucin gadi.
An kafa dokar ne domin bai wa daliban Nijeriya da ke manyan makarantun gaba da sakandare damar samun lamuni mai karancin ruwa don kammala karatunsu ba tare da sun samu tasgaro ba.