Yanzu haka dai jami’an tsaro na gumurzu da matasan da suke fasa ma’ajiyar adana Abincin kar-ta-kwana na gwamnati a jihar Adamawa.
Rahotanni sun yi nuni da cewa baya ga ma’ajiyar adana abincin matasan sun kuma ci gaba da sace kayayyankin jama’a da fasa wasu wuraren da bai shafi ma’ajiyar abincin gwamnati ba.
To sai dai jami’an tsaron ‘Yansanda suna kan kokarin ganin sun tarwatsa matasan a wurare da dama, inda suke amfani da harsashi wurin tarwatsa su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp