Jam’iyyar PDP, LP da kuma ADC sun bukaci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Mahmood Yakubu, da ya gudanar da sabon zabe.
Jam’iyyun uku a wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi a ranar Talata, a Abuja, sun yi zargin cewa zaben shugaban kasar da aka gudanar an samu tashe-tashen hankula, magudi da kuma tursasa mutane zabar wanda ba ra’ayinsu ba.
- Kotu Ta Umarci Jaridar ‘THISDAY’ Ta Biya Wike Miliyan 200 Kan Bata Masa Suna
- Peter Obi Ya Lashe Birnin Tarayya
Jam’iyyun sun bukaci da “Sashe na 60 karamin sashe na 5 na dokar zabe ya ce shugaban hukumar zai mika sakamakon zaben, gami da jimillar adadin wadanda aka tantance da kuma sakamakon kuri’u kamar yadda hukumar ta tsara.
“Rashin bin ka’idodin dokar zabe da ka’idodin ya sa ya zama dole a sabunta duk sakamakon da aka tattara a na’urar IReV kafin a sanar da gudanar da sabon zabe.
“Don haka mun bayyana cewa INEC ta yi magudin zaben tun kafin a fara tattara kuri’u a rumfunan zabe.
“INEC ta koma kan waccan alkawarin… Wannan zaben ba kwatanta gaskiya ba.
“Ba za mu kasance cikin tsarin zaben da ke gudana a yanzu haka a cibiyar tattara sakamako ta kasa ba, kuma muna bukatar a soke wannan zabe nan take.
“Muna kuma kira da a sake gudanar da sabon zabe kamar yadda INEC ta gindaya.
“Don haka muna kira ga Yakubu da ya ajiye aikinsa,” in ji shugaban jam’iyyar LP na kasa, Julius Abure, wanda ya yi jawabi da bakin jam’iyyun adawar uku.