Sanatoci a majalisar dokokin Nijeriya sun bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida don warware matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a kasar ko kuma a tsige shi.
Sanatocin sun bai wa shugaban kasa duk wani abu da yake bukata domin tunkarar kalubalen tsaro amma lamarin na ci gaba da ta’azzara har a babban birnin tarayya da fadar shugaban take.
- Da Dumi-Dumi: Sanatoci Sun Lashi Takobin Tsige Buhari Saboda Matsalar Tsaro
- Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Su Yi Hattara Da Atiku – Magoya Bayan Tinubu
Kudurin na Sanatocin ya zo ne bayan ganawar sirri ta sa’o’i biyu da shugabannin majalisar dattawa karkashin jagorancin Ahmad Lawan.
Bayan ganawar sirrin shugaban majalisar dattawan bai bai wa ‘yan majalisar damar gabatar da kudurorinsu kan shirin tsige Buhari kan rashin tsaro ba, sai dai sun yin jawabi ga ‘yan jaridu.
Shugaban marasa rinjaye na Majalisar, Aduda, ya ce a lokacin da ‘yan majalisar suka yi tattaki, “A bangaren da aka rufe mun amince da ba shi (Buhari), mun ba shi wa’adin mako shida bayan haka za mu tsige shi. Amma shugaban majalisa ya hana mu.
“Babu inda ake zaman lafiya a Nijeriya, ciki har da Abuja. Dole ne a dauki matakin gaggawa saboda haka muka fice daga zauren majalisar saboda mun bai wa shugaban kasa mako shida don ya warware matsalar ko kuma mu tsige shi.”
Sugaban marasa rinjaye na majalisar, Philip Aduda wanda ya yi magana a madadin daukacin Sanatocin ya ce “Mun bayar da duk wasu kudade, kudurori da goyon bayan da yake bukata, mataki na gaba shi ne mu tsige shi.”