Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, ya nada Alhaji Mohammadu Uba Ahmad Kari a matsayin sabon Wazirin Masarautar Bauchi.
Nadin na zuwa ne bayan tube rawanin tsohon Wazirin masarautar, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, kan zargin rashin biyayya ga gwamnan jihar, Bala Muhammad.
- 2023: Mai Binciken Kudin PDP Da Wasu Jiga-jigan Jam’iyyar Sun Koma NNPP A Gombe
- Peng Liyuan Ta Ziyarci Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Tare Da Uwargidan Shugaban Kasar Philippine
A wata sanarwar da Jami’in Watsa Labaran Masarautar, Babangida Hassan Jahun, ya fitar da yammacin ranar Alhamis, ta ce za a yi nadin ne a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce, “Majalisar Mai Martaba Sarkin Bauchi, na farin cikin gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki zuwa wajen nadin sarautar sabon Wazirin Bauchi, Alhaji Mohammadu Uba Ahmad Kari, a ranar Juma’a 6 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 11:00 na safe a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi.”
Leadership Hausa ta rawaito yadda fadar ta sanar da tsige Kirfi a matsayin Wazirin Bauchi a ranar Talata.