Sheikh Abduljabbar Nasiru kabara da ake zargi da kalaman batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi S.A.W, ya nemi a canza masa kotun da ke sauraren kararsa.
Abduljabar ya nemi Shugaban Alkalan jihar Kano, Dokta Tijjani Yusuf Yakasai, ya sauya masa kotun ne saboda zargin rashin ba shi damar kare kansa yadda ya kamata da mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ke yi.
- Darajar Naira Ta Sake Faduwa Warwas A Kan Dalar Amurka
- An Shirya Taron Farko Na Karamin Kwamitin Aikin Gona Na Kwamitin Gwamnatocin Kasashen Sin Da Najeriya
Abduljabbar wanda jigo ne a darikar Kadiriya, ya bayyana hakan ne a zaman kotun da aka yi a yau ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.
Malamin ya gabatar da bukatarsa ne bayan da kotun ta nemi sanin dalilin da ya hana lauyansa halartar zaman kotun.
Da yake bayani, Abduljabbar ya shaida wa kotun cewa ya rubuta wa shugaban alkalan Jihar, takardar neman a sauya masa kotu saboda rashin gamsuwarsa da yadda shari’ar ke tafiya da kuma yadda alkalin kotun ke mu’amala da bangarorin suka shigar da kararsa.
Sama da shekara daya ke nan, Abduljabbar na tsare a gidan yari a Kano, sakamakon zargin yin kalaman batanci da wasu malaman jihar suka ce yana yi karatunsa.