Babban Sufeton ‘Yansanda, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin kama masu sayar da sabbin takardun kudi.
Ya ce duk wadanda ke da hannu wajen siyar da takardun Naira da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sabunta.
Ya ce sun hada kafa da dukkanin jami’an tsaro don saka kafar wando da duk wanda aka kama kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.
Wannan dai na zuwa ne bayan umarnin da gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bayar na hada guiwa da jami’an EFCC da ICPC don kama masu yi wa tsarin sabbin kudin zagon kasa.
Tuni dai EFCC da ICPC suka baza jami’ansu a bankuna don sanya ido kan yadda ake hada-hadar sauya sabbin kudin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp