Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya samu lashe zaben kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu.
Tambuwal, na jam’iyyar PDP ya doke abokin takararsa na jam’iyyar APC, Ibrahim Danbaba Dambuwa, wanda shi ne Sanata mai ci.
- Karancin Kudi Na Ci Gaba Da Barazana Ga Harkokin Kasuwanci
- Al’ummar Jihar Kano Za Su Ga Sauyi Na Alkhairi A Gwamnatin Abba Gida-gida -Alhaji Abdu Kirare
Tambuwal ya samu kuri’u 100,860 yayin da shi kuma Danbaba ya samu kuri’u 95,884.
Tambuwal, wanda ya yi gwamnan jihar har sau biyu, ya kasance kakakin majalisar wakilai daga 2011 zuwa 2015 daga nan kuma aka zabe shi a gwamnan Sakkwato a zaben 2015 ya sake samun tazarce a 2019.
Dan siyasan mai shekara 57 a duniya, ya fara siyasa ne a 2003 lokacin da ya fito takarar kujerar najalisar wakilai ta tarayya da ke wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal.
Ya ci zabe da kuma zabukan da suka biyo baya a 2007 da 2011, inda ya wakilci mazabar har zuwa 2015 lokacin da aka zabe shi gwamnan Jihar Sakkwato.