A yau Talata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya fara aikinsa a fadar shugaban kasa, lamarin da ke nuni da cewa wa’adinsa ya fara aiki.
Tawagar shugaban kasar ta isa fadar gwamnatin tarayya da misalin karfe 2:35 na yammacin ranar Talata.
- Da Dumi-Dumi: An Samu Sauyin Shugabanci A Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa
- Cire Tallafin Man Fetur Ba Nan Take Zai Fara Aiki Ba, Sai Karshen Watan Yuni – Tinubu
Da isowarsa, shugaba Tinubu ya dan dakata a kofar shiga domin duba jami’an tsaro, inda ya tattauna da su kafin ya shiga cikin fadar gwamnatin.
Fitattun mutanen da suka halarci tarbar shugaban kasar sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima; Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele; Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) Mele Kyari, da Dele Alake da James Faleke.