ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wajibi Ne Japan Ta Sauke Nauyi Dake Wuyanta Kan Zuba Dagwalon Ruwan Nukiliya Cikin Teku

by CMG Hausa
3 years ago
Japan

Yayin da kasar Japan take dab da zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, Vincent Kelly, mazaunin wani tsibiri da ke tekun Pasifik ya kara bayyana damuwa, yana mai cewa, shirin Japan na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, kuskure ne, wanda zai haifar da bala’i.

Ana fatan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA da ke ziyara a Japan za ta yi bincike bisa sanin ya kamata, da adalci, a matsayin kwararriya, kan aikin Japan na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, a kokarin kiyaye tsaron kasa da kasa.

  • Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance

Tun daga jiya 29 ga wata, kwararrun hukumar IAEA suka fara ziyararsu ta kwanaki 5 a Japan. Kafofin yada labaru na Japan sun ruwaito cewa, wannan ne karo na karshe da hukumar za ta yi bincike kan aikin zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, kafin ta gabatar da rahoton nazarinta na karshe.

ADVERTISEMENT

Rafael Mariano Grossi, babban sakataren IAEA ya bayyana a fili yayin da ya ziyarci kasar Sin a kwanan baya cewa, hukumar ba ta amince ba, kuma ba ta goyon bayan shirin duk wata kasa na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, kuma ba za ta yarda da ayyukan da suka saba wa mizanin tsaro na duniya ba.

Yayin da kasashen duniya ke kin yarda da kuma nuna shakku kan shirinta na zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, bai kamata gwamnatin Japan ta nemi samun iznin zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku daga wajen hukumar IAEA ba.

LABARAI MASU NASABA

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Yau shekaru 12 da suka gabata, hadarin nukiliya na Fukushima ya haifar da babban bala’i ga duniya. Yanzu Japan tana yunkurin illata moriyar bai daya ta daukacin bil’Adama, domin samun moriyarta ta gajeren lokaci. Dole ne a ki yarda da abin da Japan take yi.

Kamata ya yi Japan ta sauke nauyin dake wuyanta, ta tattauna da kasashe makwabtanta da hukumomin kasa da kasa masu ruwa da tsaki, domin cimma daidaito. Kafin haka kuma, kada Japan ta yi gaban kanta wajen zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin teku. (Tasallah Yuan)

Japan
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola
Daga Birnin Sin

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai
Daga Birnin Sin

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
Daga Birnin Sin

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Next Post
Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Gana Da Kyari, Emefiele Kan Cire Tallafin Man Fetur

Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Gana Da Kyari, Emefiele Kan Cire Tallafin Man Fetur

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.