Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Dakta Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN).
A cewar wata sanarwa daga kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale, da ya fitar a ranar Juma’a, ta ce, Cardoso zai kasance gwamnan CBN na tsawon shekara biyar a matakin farko, amma za a tsumayi sahalewa da amincewar majalisar dattawa.
A cewarsa, “Wannan umarnin ya dace ne da sashi na 8 (1) na dokar babban bankin Nijeriya (CBN) ta shekarar 2007, da ta bai wa shugaban kasar Nijeriya karfin ikon nada gwamnan babban bankin da mataimakan gwamnan babban bankin kasa su hudu, yayin da kuma majalisar dattawan Nijeriya ke da alhakin tabbatar da nadin.
“Kazalika, shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin mataimakan gwamnan CBN su (hudu) na tsawon shekara 5 a matakin farko, amma ana tsumayar amincewa da nadin nasu daga majalisar dattawa,” ya shaida.
Sabbin mataimakan gwamnan su ne Misis Emem Nnana Usoro, Malam Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Mr. Philip Ikeazor, da Dakta Bala M. Bello.
Sanarwar ta ce, a yunkurin shugaban kasa na sabunta Nijeriya, ana sa ran wadanda aka nadan za su yi amfani da kwarewarsu da gogewarsu wajen kyautata ayyukansu da kuma taimakawa wajen bunkasa harkokin tattalin arziki kamar yadda ‘yan Nijeriya ke tsammata.
LEADERSHIP ta labarto cewa tun lokacin da aka danatar da Mista Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN a watan Yuni, mataimakin gwamnan bankin, Faloshodun Shonubi, ke jagorantar ragamar babban bankin na kasa har zuwa wannan matakin da Tinubu ya nada sabon gwamnan da mataimakansa hudu.